’Yan sandan Kano sun kama mutane uku da ake zargi da hannu a kisan wata uwa da ‘ya’yanta shida a Dorayi Chiranchi. Dan ’yar uwar marigayiyar na daga cikin wadanda aka kama.
Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Kano ta tabbatar da kama mutane uku da ake zargi da hannu a kisan wata uwa da ‘ya’yanta shida a unguwar Dorayi Chiranci lamarin da ya girgiza al’ummar yankin.
Sanarwar kamen na kunshe ne cikin bayanin da kakakin rundunar ’yan sanda ta jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar a ranar Lahadi, inda ya bayyana cewa an gudanar da aikin ne bisa sahihan bayanan sirri da rundunar ta samu.
A cewar rundunar, an aiwatar da samamen ne karkashin umarnin Sufeto Janar na ’Yan Sanda, Kayode, tare da kulawar Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Kano, Ibrahim Adamu Bakori
Lokacin da Aka Yi Kamen
Rundunar ta ce an gudanar da samamen ne daga karfe 10:00 na dare a ranar 17 ga Janairu zuwa karfe 4:00 na asubahin ranar 18 ga Janairu, 2026, inda aka samu nasarar cafke waɗanda ake zargi ba tare da wata tangarda ba.
Sunayen Wadanda Aka Kama
Mutanen da aka kama sun hada da:
- Umar Auwalu (mai shekaru 23) daga unguwar Sabuwar Gandu
- Isyaku Yakubu wanda aka fi sani da “Chebe” (mai shekaru 40) daga unguwar Sagagi
- Yakubu Abdulaziz wanda aka fi kira “Wawo” (mai shekaru 21) daga unguwar Sabon Gida Sharada
’Yan sanda sun bayyana cewa Umar Auwalu, wanda ake zargin jagorantar kisan kuma dan ’yar uwar marigayiyar ne, ya amsa hannu a laifin.
Abubuwan da Aka Kwato
Daga cikin kayayyakin da aka kwato daga hannun wadanda ake zargin akwai:
- Tufafi masu tabon jini
- Wayoyin salula biyu na marigayiyar
- Adda da gora
- Kuɗi da ake zargin an kwace daga wajen da abin ya faru
- Wasu makamai masu haɗari
Rundunar ta ce bincike na ci gaba domin gano ko akwai wasu da ke da hannu a laifin.
’Yan Sanda Sun Yi Alkawarin Gurfanarwa
Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Kano ta yaba wa jami’an da suka gudanar da aikin, tare da gode wa al’umma kan addu’o’i, goyon baya da haɗin kai. Rundunar ta kuma jaddada ƙudirinta na ganin an gurfanar da duk wanda aka samu da laifi a gaban kotu domin ya fuskanci hukunci bisa doka.
