API

Dr. Abbas Tajudeen, ya bayyana matukar damuwa game da rasuwar Sheikh Usman Idris Kusfa.

Kaduna - Shugaban Majalisar Wakilai Dr Abbas Tajudeen, ya bayyana matukar bakin ciki game da rasuwar malamin addinin Musulunci mazaunin Zariya, Sheikh Usman Idris Kusfa, wanda aka fi sani da Rigi-Rigi.



Shugaban Majalisar Wakilai Abbas, a cikin sakon ta'aziyya ta hannun Mai Ba shi Shawara na Musamman kan Kafafen Yada Labarai, Musa Abdullahi Krishi, ya ce ya sami labarin rasuwar Sheikh Usman Idris Kusfa, wanda aka fi sani da Rigi-Rigi, cikin matukar mamaki.

Ya bayyana marigayi malamin Tijjaniya a matsayin sanannen shugaban addini, wanda ya yi amfani da ilimin da Allah Ya ba shi wajen yada addinin Musulunci, inda ya gina al'umma mai adalci a addini.

Shugaban Majalisar Wakilai Abbas ya yi addu'ar Allah Ya jikan marigayi Sheikh Usman Kusfa, yana mai cewa, "Allah Ya gafarta masa kurakuransa Ya kuma ba shi mafi kyawun matsayi a Jannatul Firdaus."

Fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Usman Kusfa, wanda aka sani da hanyar koyarwa ta musamman, ya rasu a daren Lahadi a Kaduna, yana da shekaru 57.


- Hajara Balarabe