API

Search

EFCC Ta Ci Gaba da Tsare El-Rufai, Yayin DSS ke Dakonsa

 EFCC Ta Ci Gaba da Tsare El-Rufai, DSS Na Ci Gaba da Bincike Kan Zargin Kutsen Wayar Ribadu


Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ƙasa, EFCC, na ci gaba da tsare tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, bayan gayyatarsa da ta yi domin amsa tambayoyi kan zargin badakalar kuɗi da ya kai naira biliyan 432.



Majiyoyi daga cikin hukumar sun ce ana ci gaba da yi masa tambayoyi kan yadda aka tafiyar da wasu kuɗaɗen gwamnati a lokacin mulkinsa, yayin da ake tattara ƙarin hujjoji kan zargin.


A lokaci guda kuma, DSS ta ce tana gudanar da bincike kan zargin da El-Rufai ya yi na cewa ana satar bayanan wayar mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu.


El-Rufai ya yi wannan ikirari ne a wata hira da ya yi da Arise TV, inda ya ce akwai alamun ana bibiyar wayoyin wasu manyan jami’an gwamnati. DSS ta bayyana cewa binciken nata zai gano gaskiyar zargin tare da ɗaukar matakin da ya dace idan an tabbatar da wani laifi.


Har zuwa yanzu, babu wata sanarwa a hukumance daga ɓangaren El-Rufai kan ci gaba da tsare shi, yayin da lamarin ke jawo muhawara a faɗin Nigeria.


Za mu ci gaba da kawo muku sabbin bayanai yayin da ake samun su.