API

Search

Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya gana da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a Fadar Shugaban Kasa

Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya gana da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja domin tattauna batutuwan tsaro da ci gaba a jihar.


Gwamnan ya yi wa Shugaban Kasa bayani kan ceto masu ibada da aka sace daga coci-coci a garin Kurmin Wali na Karamar Hukumar Kajuru lamarin da Faru a  ranar 18 ga Janairu shekarata 2026.

Ya ce an ceto wadanda abin ya shafa lafiya ta hanyar hadin gwiwa da hukumomin tsaro na jiha da na tarayya 

Gwamna uba Sani ya kuma godewa Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu saboda goyon bayan da ya bayar  a lokacin sace mutanen.

Ganawar ya kuma duba muhimman ayyukan tituna, ciki har da titin Birnin Gwari a hanyar Kaduna ta Gabas da titin Jere Zuwa Kwoi Wanda ta nufi Kafanchan da titin Zaria  Zuwa Pambegua Wanda ta nufi Saminaka.

Gwamnan ya sake jaddada kudirin Jihar Kaduna na yin aiki tare da Gwamnatin Tarayya don inganta tsaro da ci gaba.


- Hajara Balarabe