API

Search

Gwamnatin Amurka ta ƙaƙaba takunkumai kan wasu ‘yan Nijeriya 18 da wasu ƙungiyoyi

Gwamnatin Amurka ta ƙaƙaba takunkumai kan wasu ‘yan Nijeriya 18 da ƙungiyoyi daban-daban bisa zargin hannu a ta’addanci, laifukan intanet, da safarar miyagun ƙwayoyi.

Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da Washington ke ƙarfafa haɗin gwiwar soji da Nijeriya domin daƙile barazanar masu tsattsauran ra’ayi.

A ƙarƙashin shirye-shiryen ofishin Amurka mai kula da kadarori na ƙetare (OFAC), an ayyana waɗannan mutane da ƙungiyoyi a matsayin Specially Designated Global Terrorists (SDGT), waɗanda ke da alaƙa da intanet (CYBER2), da kuma masu safarar ƙwayoyi (SDNTK).




Boko Haram da ƙungiyoyin IS

Cikin waɗanda aka sanya wa takunkumi akwai tsohon shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau, da kwamandojin da ke da alaƙa da IS, Abu Musab al-Barnawi da Khalid al-Barnawi, tare da wasu masu hulɗa da su. Wannan ƙungiyoyin sun shafe fiye da shekaru goma suna kai hare-hare a arewa maso gabashin Nijeriya.

Haka kuma, an ƙara wasu ‘yan Nijeriya kamar Salih Yusuf Adamu, Ibrahim Ali Alhassan, Surajo Abu Bakr Muhammad, Abdurrahman Ado Musa, da Ali Abbas Usman Jega.

Bugu da ƙari, an sanya takunkumi kan reshen Nijeriya na ƙungiyar RIHS, wadda ake zargin tana taimaka wa ayyukan masu tsattsauran ra’ayi.


Laifukan intanet da safarar ƙwayoyi

A wani mataki daban, an bayyana wasu ‘yan Nijeriya biyar — Nnamdi Orson Benson, Abiola Ayorinde Kayode, Alex Afolabi Ogunshakin, Micheal Olorunyomi, da Richard Izuchukwu Uzuh — a ƙarƙashin dokar hana laifukan intanet ta Amurka (US CYBER2) saboda zargin rawar da suka taka wajen shirya manyan damfara ta intanet.

Haka kuma, mutane biyu — Wole A. Ogungbuyi da Babestan Oluwole Ademulero — an ayyana su a matsayin manyan masu safarar miyagun ƙwayoyi bisa zargin su na kasancewa cikin masu safara a matakin duniya.