API

Gwamnatin Jihar Kogi ta rufe makarantu na wucin gadi a fadin jihar.

Da yake magana da manema labarai a Lokoja, Kwamishinan Yaɗa Labarai da Sadarwa na Jihar, Kingsley Femi Fanwo, ya bayyana cewa an yanke shawarar hana yaɗuwar cutar ne bisa ga sahihan bayanan sirri da kuma buƙatar sanya matakan kariya a kusa da makarantu don kare ɗalibai,da malamai.


Ya ce, Gwamnan Jihar Ahmed Usman Ododo ya kuma umarci dukkan hukumomin da abin ya shafa da su gaggauta amfani da hanyoyin da suka dace don tabbatar da cewa makarantu sun ci gaba da gudanar da ayyukan ilimi da zarar sun kasance lafiya, don kada su wargaza kalandar ilimi ta jihar.


Fanwo ya yaba wa hukumomin tsaro bisa ga bayanan sirrin da suka bayar a kan lokaci da kuma wanda za a iya aiwatarwa, yana mai lura da cewa irin wannan haɗin gwiwa yana nuna ingancin tsarin tsaron jihar.


Ya tabbatar wa mutanen Jihar Kogi cewa gwamnati tana kan gaba wajen shawo kan lamarin, ya ƙara da cewa hukumomin tsaro sun riga sun fara aiki ba dare ba rana don gano da kuma magance maɓoyar masu laifi.


- Hajara Balarabe