API

Search

Gwamnatin Tarayya ta amince da sake bude iyakar Tsamiya a Jihar Kebbi

Gwamnatin Tarayya ta amince da sake bude iyakar Tsamiya a Jihar Kebbi don cinikin kan iyakoki, tare da tsauraran matakan tsaro da bin ka'idoji.

Kwamanda Janar na hukumar Kwastam Adewale Adeniyi, ya bayyana hakan ne yayin da yake mayar da martani ga damuwar da masu ruwa da tsaki, ciki har da masu fitar da kaya da masu sufuri da masu sayar da albasa, suka nuna, a wani zaman tattaunawa a Jihar Kebbi.



Ya tabbatar wa masu gudanar da harkokin tattalin arziki cewa Gwamnatin Tarayya ba ta damu da wahalar da aka sha sakamakon tsawaita takunkumin kan iyakoki ba, yana mai lura da cewa matsalar ta shafi manyan jami'an diflomasiyya da tsaro da hukumar kwastam a fadin Najeriya da kasashen makwabta.

Shugaban hukumar Kwastam ya bayyana cewa Najeriya ta karbi tawagar gaggawa daga Hukumar Kwastam ta Jamhuriyar Nijar da membobin Cibiyar Kasuwanci da ke Abuja don hanzarta magance matsalar cinikayya.



A cewarsa, shawarar sake bude hanyar Tsamiya ta biyo bayan kudurin siyasa mai karfi daga Shugaban kasa Bola Tinubu don hadin gwiwa daga gwamnatocin makwabta.

Kazalika hukumar Kwastam za ta tura tsarin sadarwa mai Amfani da fasahar zamani daga hukumomin kwastam a Jamhuriyar Benin da Nijar don tabbatar da sa ido da kuma bayyana gaskiya.  

Adeniyi, ya kuma yi gargadin cewa za a kwace kayan da aka haramta amfani da su a cikin sufuri, sannan kuma za a kwace manyan motoci da aka samu a wajen kar'ya dokokin sufuri da aka amince dasu