Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta kammala jadawalin zaɓenta da jadawalin ayyukan babban zaɓen 2027, duk da ci gaba da jinkirin da ake samu wajen amincewa da gyaran Dokar Zaɓe da Majalisar Dokoki ta Ƙasa ta yi.
Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, ya bayyana hakan a Abuja yayin tarurruka daban-daban da shugabannin kafofin watsa labarai da ƙungiyoyin fararen hula.
Ya lura cewa yayin da hukumar ta gabatar da buƙatunta ga Majalisar Dokoki ta Ƙasa, wasu ɓangarori na jadawalin na iya shafar lokacin da dokar zaɓe za ta ɗauka.
Farfesa. Amupitan ya jaddada cewa INEC a halin yanzu tana dogara ne da Dokar da ke akwai don ayyukanta, yayin da take jiran shawarar Majalisar Dokoki ta Ƙasa.
An kammala Jadawalin da Ayyuka na Babban Zaɓen 2027 bisa ga cikakken bin Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Najeriya, 1999 (kamar yadda aka gyara), da Dokar Zaɓe, 2022,"
Amupitan ya kuma jaddada cewa sahihancin masu zaɓe miliyan 93.4 da aka yi wa rijista a halin yanzu abin fifiko ne.
- Hajara Balarabe Musa