API

Search

Jami'an DSS sun sake kama Nasir El-Rufai bayan EFCC ta sake shi

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya sake fadawa hannun jami’an tsaro na DSS jim kaɗan bayan Hukumar EFCC ta gama yi masa tambayoyi ta kuma sake shi.

Jaridar Premium Times ta wallafa rahoton cewa jami’an Hukumar Tsaro ta DSS ne suka karɓe shi daga ofishin EFCC domin ci gaba da bincike a kansa kan wasu zarge-zargen laifukan yanar gizo.

Tun farko EFCC ta tsare El-Rufai ne bisa zargin karkatar da kudaden gwamnati da ake danganta wa da mulkinsa na gwamna a Kaduna daga 2015 - 2023.


Hukumar ta gayyace shi domin amsa tambayoyi, inda ya bayyana cewa ya amsa gayyatar ne da kansa.

Sai dai bayan an sake shi, jami’an DSS suka kama shi domin fuskantar tuhuma kan zargin kutsawa cikin sirrin wayar jami’an gwamnati ba bisa ka’ida ba, wanda ake zargin ya fito ne daga kalaman da ya yi a wata hira ta talabijin.

Ana sa ran za a gurfanar da shi a gaban kotun tarayya da ke Abuja kan wadannan tuhume-tuhume, yayin da bincike kan zargin cin hanci da rashawa da EFCC ke yi a kansa ke ci gaba.

Lamarin ya janyo cece-kuce a fagen siyasar Najeriya, inda magoya bayansa da masu adawa da shi suka yi zanga-zanga a wajen ofishin EFCC a lokacin da yake tsare.