API

Jihohi 26 Ba Za Su Iya Biyan Albashi Ba Ba Tare Da Asusun Tarayya — Ministan Yaɗa Labarai

 Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Ƙasa, Mohammed Idris, ya ce jihohi ashirin da shida daga cikin 36 na Najeriya ba za su iya biyan albashin ma'aikata ba tare da an ware musu asusun Tarayya ba.




Ya bayyana hakan ne yayin da yake gabatar da lacca ta 34 kafin taron jami'a na Jami'ar Fasaha ta Tarayya (FUT), Minna, mai taken "Gina Matasa da Ƙasa: Kewaya Damar Aiki a Zamanin Gyaran Ƙasa."


Ministan ya ce gyare-gyaren da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi suna haifar da sakamako, yana mai lura da cewa yanzu jihohi suna samun ninki biyu ko ma sau uku na kuɗin da suka kashe a baya, yana mai ƙara da cewa babu wani gwamna da zai iya ɗora alhakin ƙalubalen albashi akan rashin kuɗi.


Idris ya kuma bayyana cewa an raba sama da biliyan ₦174 ta hanyar NELFUND don biyan kuɗin makaranta da kula da yara, yana mai kira ga waɗanda suka kammala karatun su yi amfani da damar gwamnati, yayin da Najeriya ke ɗaukar kanta a matsayin cibiyar zuba jari, kirkire-kirkire, da ci gaban matasa.


- Hajara Balarabe Musa