Shugaban ƙasar Nijar, Janar Abdourahamane Tiani, ya isa Aljeriya ranar Lahadi a wata ziyara ta aiki, inda ya gana da Shugaba Abdelmadjid Tebboune. Wannan ganawa na nuna ƙarshen sama da watanni 10 na rashin jituwa tsakanin Nijar da Aljeriya.
Fadar shugaban Aljeriya ta ce Tebboune ya karɓi Tiani tare da babban tawagarsa, inda aka gudanar da tarbar faretin ban-girma a filin jiragen sama na Houari Boumediene, Algiers. Gidan talabijin na ƙasar ya bayyana ziyarar a matsayin alamar “zurfin alaƙa ta tarihi” tsakanin ƙasashen biyu.
Manyan jami’an Aljeriya sun halarci tarbar, ciki har da kakakin majalisar dokoki Azzouz Nasri, Hafsan Soji Janar Said Chanegriha, Ministan Harkokin Waje Ahmed Attaf, da Ministan Ma’adinai Mohamed Arkab. Tebboune da Tiani sun yi tattaunawa ta musamman, duk da cewa ba a fitar da bayanai kan tsawon ko abinda aka tattauna ba.
Tarihin Rashin Jituwa
Rashin jituwar diflomasiyya ya fara ne tun watan Afrilu, lokacin da Nijar, Burkina Faso da Mali suka kira jakadunsu daga Aljeriya. Wannan ya biyo bayan zargin Mali cewa jirgi daga Aljeriya ya ketare sararin samaniyarta. Aljeriya ta mayar da martani ta hanyar kiranye jakadunta daga ƙasashen uku, inda ta ce matakin Nijar ya samo asali ne daga matsayin ta a ƙungiyar Sahel AES, ba rikici kai tsaye ba.
Alamu na Karshen Rikici
A ƙarshen shekarar da ta gabata, alamun raguwa sun fara bayyana. A watan Nuwamba, shugaban Nijar ya aika saƙo ga Tebboune game da ranar tunawa da juyin-juya-halin Aljeriya. A watan Janairu, Ministan Makamashi na Aljeriya, Mohamed Arkab, ya ziyarci Nijar domin duba ayyukan haɗaka na mai.
Nijar da Aljeriya suna da kan iyaka mai tsawon kilomita 950 kuma suna haɗa kai kan muhimman ayyuka na yanki, ciki har da babban titin Hamadar Sahara da shirin samar da bututun gas wanda zai kai iskar gas daga Nijeriya zuwa Turai ta Nijar da Aljeriya. Wannan aiki zai ba da damar tura kubik mita biliyan 30 na iskar gas a kowace shekara.
