Jamhuriyar Nijar ta nuna bacin rai kan kudurin Majalisar Tarayyar Turai na neman a saki tsohon shugaban kasa Mohamed Bazoum, matakin da hukumomin Nijar ke kallon sa a matsayin tsoma baki cikin harkokinsu.
Rahoton DW ya ce ministan harkokin wajen Nijar, Bakary Yaou Sangare, ya mika wa wakiliyar Tarayyar Turai wasika mai dauke da korafi kan kudurin da ‘yan majalisar Turai suka amince da shi. Kudurin ya bukaci a saki Bazoum tare da kara matsin lambar diflomasiyya domin kawo karshen tsarewarsa.
A gefe guda, masu adawa da gwamnatin sojan Nijar sun ce matakin Turai abin maraba ne, yayin da wasu masu sharhi ke ganin sabuwar guguwa ce ta diflomasiyya da za a iya shawo kanta daga baya. Sai dai rahoton ya nuna cewa sabuwar takaddamar na iya jefa dangantakar Nijar da Turai cikin wani sabon yanayi na tsamiya.
Madogara: DW Hausa
