API

Search

Tinubu ya gana da hafsoshin tsaro kan sabbin hare-hare

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gana da manyan hafsoshin tsaron Najeriya domin tattauna sababbin hanyoyin dakile matsalolin tsaro da suka sake tsananta a sassan kasar.




DW ta ruwaito cewa karuwar hare-haren da ake kai wa sansanonin soja cikin makwannin baya ne ya sa aka dauki wannan mataki na gaggawa. Bayanai sun nuna cewa mayaƙan ISWAP sun kai farmaki a sansanoni da dama, lamarin da ya tayar da hankalin jami'an tsaro da gwamnati.


A cewar jami'an gwamnati da masu sharhi kan tsaro, ana bukatar sababbin dabaru domin hana sake tabarbarewar lamarin. Duk da nasarorin da sojoji ke cewa sun samu a wasu gurare, rahoton ya nuna cewa har yanzu kalubalen tsaro ya kasance babbar matsala bayan shekaru 17 na fada da kungiyoyin masu tayar da kayar baya da ‘yan bindiga.


Madogara: DW Hausa