API

Search

Trump ya ce bai gamsu da sharuddan sasanci da Iran ba

Donald Trump ya ce Iran na nuna sha'awar sasanci, amma a cewarsa har yanzu bai gamsu da sharuddan da ake kokarin shimfidawa domin cimma yarjejeniya ba.




A hirarsa da NBC ta wayar tarho ranar Asabar, Trump ya ce duk wata yarjejeniya da za a kulla dole ne ta kunshi janyewar Iran daga duk wani buri na mallakar makamin nukiliya. Sai dai bai fayyace sauran sharuddan da yake nufi ba.


Ya kuma yi ikirarin cewa harin da Amurka ta kai ranar Juma'a ya lalata tsibirin Kharg, wata muhimmiyar cibiyar fitar da man Iran. A lokaci guda, Iran ta ci gaba da kai hare-hare a sassan Gabas ta Tsakiya da kuma Isra'ila, abin da ya sa Amurka ta gargadi ‘yan kasarta da su fice daga wasu kasashen yankin cikin gaggawa.


Rahoton ya nuna cewa kalaman Trump sun saba da wasu bayanansa na baya da suka takaita harin Amurka zuwa sansanonin soji kawai. Yayin da rikicin ke kara kamari, ana ci gaba da fuskantar rashin tabbas kan ko sasanci zai yiwu nan kusa ko kuma bangarorin za su kara tsaurara matsayinsu.


Madogara: BBC Hausa